A Najeriya Sallar azumi ya gudana cikin lumana
August 30, 2011An gudanr da bukuwan Sallar azumi cikin zullumi da fargaba a wasu jihohin Arewacin Najeriya, abinda ya haifar da tsauraran matakan tsaro a kusan dukkanin jihohin kasar fiye da yadda aka saba a baya, inda a bangare guda kuma al'ummomi suka koka saboda halin kunci da sallar ta bana ta zo da shi.
Ganin irin hare-haren da aka kai a ‘yan kwanakin nan da kuma rahotannin sirri da aka samu na yiwuwar kai hare-hare ko dai na bom ko na bindigogi, an tsaurara matakan tsaro a sassan jihohin Arewacin Najeriya yayinda musulmai ke bukukuwan sallah.
Ga misali a birnin Maiduguri mai fama da hare-haren bama bamai da bindigogi an kara yawan shingayen bincike motoci da kuma yawan jami'an tsaro tare da tsare manyan hanyoyin birnin.
Haka kuma an samar da jiragen masu tashin ungulu da suke shawagi kan sararin samaniyar garin, kari bisa motocin sintiri da ke zirga-zirga a kasa.
Haka al'amarin ya ke a sauran jihohi da ke makobtaka da jihar Borno, jami'an tsaro sun ja daga a wurare da dama tare da yin sintiri a motoci don tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma.
Matakan da jami'an tsaron suka dauka sun jefa tsoro a zukatan masallatan inda da dama suka yi sallar cikin zullumi.
Bisa taimakon Allah dai an yi sallar lami lafiya inda har ya zuwa lokacin wakilinmu Amin Sulaiman ya kamala hada rahoton da ya aiko mana ba a samu rahoton barkewar rikici ko wani hari ba a dukkanin jihohin Arewa maso gabashin Najeriya.
Babbar matsalar dai ta zo wa al'umma a sallar, ita ce ta rashin walwala abinda ake dangantawa da karancin masu gidan rana a hannun jama'a ba kamar yadda suka saba a baya ba.
Haka kuma ma'aikata da dama sun yi sallah ba tare da samun albashi ba, duk da cewa watan ya kare abinda ya haifar da takura da rashin annuri a fuskokin jama'a, wannan kuma ya rage armashi da tagomashin sallar ta bana.
Ko daga irin kayan ado da jama'a suka sa a wannan rana musamman yara za'a iya gane cewa sallar ta bana babu harka. Masu iya magana dai na cewa Sallah mai dogon baya ta tafi ta bar wawa da bashi, amma wannan karo jama'a da dama bashi suka ci suka yi don fita kunyar bukin Sallar.
Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita:Usman Shehu Usman