Babbar jam'iyyar adawa ta Jamhuriyar Nijar ta shiga rikici
July 26, 2019Kotu ta bai wa shugaban riko Oumarou Noma gaskiya kan korar shi da Hama Amadou Ya yi daga mukaminsa na shugaban riko na Jam’iyyar ta Lumana. Sai dai wannan hukunci ya buda wani sabon babi na rikicin cikin gida a babbar jam’iyya ta adawa.
Hukuncin dai na kotu ya yi watsi da hujjojin da lauyoyin Hama Amadou suka bayar na cewa dokokin jam’iyyar ba su ba da izinin kai kara a kotu ba sai an nemi gyara lamarin a cikin jam’iyya. Kotun ta ce ta yi amfani ne da cewa tun lokacin da aka yanke wa Hama Amadou hukuncin dauri na shekara daya da kudiri mai lamba 31/ 17 na ranar 13 ga watan Maris na 2017 na kotun daukaka kara ta Yamai, Hama Amadou ba shi da izinin shugabancin jam’iyya, kuma ba shi da hurumin korar shugaban riko Oumarou Noma daga wannan mukami. Tuni dai zukata suka harzuka a bangaren magoya bayan Hama Amadou da ke cewa za su dauki mataki.
Wannan rikici dai na jam’iyyar Lumana Afirka ya dauko sali tun da jimawa, inda lokacin da aka bayar da hukuncin dauri ga shugaban Jam’iyyar Hama Amadou sakamakon shari’ar nan ta safarar jarirrai, aka yi ta jin wasu maganganu na cewa akwai masu bukatar samun wannan kujera ta jagorancin jam’iyyar. Sai dai kuma a duk lokacin da suka yi taro magoya bayan jam’iyyar na jaddada goyon bayau ga Hama Amadou da cewa shi ne zai kasance dan takara.
Lauyoyin bangarorin biyu sam sun ki cewa uffan. Sai dai ga labarin da muka samu dai kwamitin koli na jam’iyyar ta Lumana Afirka zai yi wani zaman taro na gaggawa domin duba wannan lamari, kafin daga bisani su fitar da sanarwa, yayin da a hannu daya ake cewa lauyan na Hama Amadou Barista Mossi ya daukaka kara kan hukuncin, lamarin da ke nunin cewa an kama wata sabuwar hanya ta hayaniyyar siyasa a cikin jam’iyyar ta Lumana Afirka ta Hamma Amadou tsohon shugaban majaliyar dokoki kana tsohon firaminista da ke gudun hijira a kasar Faransa kusan shekaru biyar ke nan.