A Ghana jam'iyar NPP ta shigar da kara a kotu
December 28, 2012Talla
Babbar jam'iyar adawa a kasar Ghana ta shigar da kara a kutu, inda take kalubalantar zaben da ya baiwa shugaba John Mahama nasara. A karar da jam'iyar NPP ta shigar a kotun kolin kasar, ta yi zargin cewa an tabka magudi a zaben ya gabata. Mahama ya samu nasarar sama da kashi 50 cikin dari a yawan kuri'un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar Ghana ta sanar. Inda hukumar tace madugun yan adawa Nana Akufo-Addo ya zo na biyu da sama da kuri'u kashi 47 cikin dari. Kasar Ghana mai yawan al'umma miliyan 25 itace ake ganin daya daga kasashen Afirka kalilan da ke dan tsarin demokradiyya mai inganci a Afirka.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi