1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fama da karancin abinci a Sudan ta Kudu

Binta Aliyu Zurmi MAB
April 9, 2022

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi nuni da cewar akalla al'ummar kasar miliyan 8 na fuskantar matsalar karancin abinci a yayin da rikicin kasar ke kara ta'azzara.

https://p.dw.com/p/49iJz
Südsudan l Krise l Hunger - Kinder in Juba
Hoto: Tony Karumba/AFP via Getty Images

A sanarwar hadin gwiwa da mahukuntan kasar Sudan ta Kudu gami da Majalisar Dinkin Duniya suka fidda a wannan Asabar ta nuna yadda sama da kaso 60 na cikin dari na al'ummar kasar ke cikin hali na 'yunwa da ke da nasaba da tashe-tashen hankula da kuma iftila'i da kasar ke fuskanta.

Kasar ta Sudan ta Kudu da ke zama jaririyar kasa ta jima tana fama da matsaloli tun bayan samun 'yancin a shekarar 2011, lamarin da ya kai ta ga kwashe tsawon shekaru a cikin yakin basasa. Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakin matsalolin da kasar ke fuskanta musamman ma na siyasa a kan shugaban kasar Salva Kiir da madugun adawa Riek Machar.