2023: 'Yan Media sun ce za su daina tallan APC
November 22, 2022Tun a baya dai matasan 'yan media sun dade suna ta korafi kan irin yadda suka ce suna tura mota amma daga karshe ta bule su da hayaki, amma wannan korafi nasu ya kara bayyana sosai bayan da jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Filato da ke tsakiyar kasar.
Matasan suka ce tsarin da aka bi wajen kai takwarorinsu 'yan fim Filato din a jirgin sama, su kum aka kaisu a motocin haya abin takaici ne. Wannan batu dai ya sanyasu yin tutsu har ma shugaban kungiyarsu na arewacin Nigeria Rabiu Biyora ya saki sanarwar cewar sun tsaya cak yada manufofin jamiyyar APC.
A daura da wannan batu, guda daga cikin 'yan media din wanda yanzu yake kan kujerar shugabancin karamar hukumar Nasarawa a Kano, Auwal Lawal Aronposu, ya ce masu wannan kuka wadanda su ka yi yakin neman zaben shugaban kasa ne a baya ba a yi rabon mukamai da su ba kuma ya ce suna da dalilin kokawa.
Da yake maida martani kan wannan batu, hadimin shugaban kasa Buhari a kan kafafen sada zumunta kuma mataimakin daraktan yakin neman zaben Bola Ahmad Tinubu na kafafen yada zumunta, Bashir Ahmad, ya ce ba a mai da masu korafin 'yan bora ba don wasu daga cikinsu sun amfana sosai.
A share guda kuma Mustapha Badamasi Naburaska wanda dan fim ne kuma ake dama da shi a gwamnatin Kano ya ce kansu a hade yake kana ana kula da kowa. Duk da cewar 'yan kungiyar sun tsya cak sun daina yada manufofin jam'iyya amma wata majiya ta tabbatar da cewar an gano bakin zaren nan gaba kadan ma za su janye wannan barazana.