Ɗan China Liu ya samu kyautar Nobel
October 8, 2010A bana ɗan ƙasar Chinan nan mai radin kare haƙin ɗan Adam, Liu Xiaobo ya samu kyautar zaman lafiya ta Nobel. A lokacin bikin sanarwar, shugaban kwamitin kyautar Nobel Thornjorn Jagland ya ce an zabi Liu ne saboda gwagwarmayarsa ta kare haƙin ɗan Adam.
"Kwamitin Nobel a ƙasar Norway ya yanke shawarar ba da kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shekarar 2010 ga Liu Xiaobo saboda doguwar gwagwarmayar tabbatar da kare 'yancin Bil Adama a China ba tare da tashin hankali ba."
Xiaobo ɗan shekaru 54 a duniya wanda aka taɓa ɗaure shi a kurkuku saboda shiga cikin zanga-zangar neman demokuraɗiyya ta Tiananmen a shekarar 1989, an sake yanke masa hukuncin shekaru 11 a kurkuku a cikin watan Disamba bisa laifin yiwa gwamnati zagon ƙasa. A cikin shekarar 2008 aka kame shi bayan yayi kira da aiwatar da sauye sauyen siyasa da haƙin ɗan Adam a China mai bin tsarin kwaminisanci.
Gwamnatin China dai ta fusata matuƙa dangane da kyautar zaman lafiya ta Nobel da aka bawa bijirarren ɗan ƙasarta, Liu Xiaobo wanda a halin yanzu yake ɗaure a kurkuku. A cikin martanin da ta mayar ma'aikatar harkokin wajen China a birnin Beijing ta ce ba da irin wannan kyautar ga wanda ake tsare da shi abin kunya ne da ba za a amince da shi ba. To sai dai gwamnatocin ƙasashen Turai ciki har da Jamus da Faransa sun yaba da wannan kyautar suna masu yin kira ga gwamnatin China da sako Liu domin ya samu sukunin zuwa karɓar kyautar da kansa. Shi ma shugaban hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya yi lale maraba da wannan matakin a matsayin wani babban goyon baya ga masu gwagwarmayar neman 'yanci da kare haƙin Bil Adama a duniya baki ɗaya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu